• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Ɗaure Wani Mutum Kan Zargin Cin Mutuncin Limami A Kano

by Naziru Adam Ibrahim
1 year ago
Kotu

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare wani Malam Nasiru Mukhtar, bisa zargin cin zarafin Limamin wani Masallaci da ke Tudun wada. 

Ana zargin Mukhtar da shiga Masallacin tare da kai wa Limamin Malam Murtala Sulaiman, hari yayin da yake shirin jan sallar Asuba, a ranar 22 ga watan Oktoba, 2024.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na Asuba, inda Mukhtar ya shiga Masallacin tare shaƙe Limamin.

Kazalika, ya kama shi da damɓe da yayyaga rigarsa, sannan ya lalata na’urar amsa kuwwar limamin, lamarin da ya sa shi kai rahoto ga rundunar ‘yansandan Jihar Kano.

Rundunar ‘yansandan ta shaida cewa tuhumar da ake yi wa Mukhtar, ta yi daidai da sashe na 165 da 166 na kundin laifuka na jihar.

LABARAI MASU NASABA

Matashi Ya Kashe Ɗan Acaɓa Don Neman Kuɗin Auren Mace Ta Uku A Bauchi

Matashi Ya Kashe Kakanninsa Kan Abinci A Kano

Amma wanda ake tuhumar ya musanta laifin lokacin da lauyan mai shigar da ƙara Aliyu Abidin, ya karanta masa tuhumar a gaban kotu.

Daga ƙarshe Alƙalin kotun, Malam Isah Rabi’u Gaya, ya yi watsi da buƙatar neman belin wanda ake ƙara, tare da bayar da umarnin gwajin lafiyar wanda ake zargin a wani asibiti da ke yankin don tantance lafiyar ƙwaƙwalwarsa.

Alƙalin ya bayar da umarnin a tsare Mukhtar, tare da ɗage shari’ar zuwa 22 ga watan Nuwambar 2024, don ƙara bincike.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Al'ajabi

Matashi Ya Kashe Ɗan Acaɓa Don Neman Kuɗin Auren Mace Ta Uku A Bauchi

October 17, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano
Al'ajabi

Matashi Ya Kashe Kakanninsa Kan Abinci A Kano

September 25, 2025
Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
Al'ajabi

Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye

September 17, 2025
Next Post
Mene Ne Burin Amurka Wajen Sake Yada Jita-Jitar “Barazanar ‘Yan Leken Asirin Kasar Sin”

Mene Ne Burin Amurka Wajen Sake Yada Jita-Jitar “Barazanar ‘Yan Leken Asirin Kasar Sin”

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.