Wata Kotun Majistare da ke Kano ta bayar da umarnin a tura Ashiru Idris, wanda aka fi sani da Mai Wushirya, gidan gyaran hali na tsawon mako biyu saboda wallafa bidiyon batsa da ya shafi budurwa (dwarf) da ba a bayyana sunanta ba, a dandalin sada zumunta.
Mai shari’a Halima Wali ta Kotun Majistare mai lamba 7 ce ta bayar da wannan umarni, tana mai cewa a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali kafin a dawo da ƙarar don ci gaba da sauraro.
- Kotu Ta Yanke Wa Ɗan TikTok Tsulange Hukuncin Ɗauri Kan Shigar Zubar Da Mutunci
- Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok
Hukumar kula finafinai da ɗab’i ta jihar Kano ce ta kama Mai Wushirya makon da ya gabata bayan da wasu bidiyoyi na rashin kunya suka yaɗu a intanet, inda aka gan shi ba tare da riga ba yana aikata abin da hukumomi suka bayyana a matsayin “abin kunya da rashin mutunci.”
Mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya ce kotu ta umarci a kawo matar da ta fito a cikin bidiyon kafin a ci gaba da shari’ar, yana mai bayyana cewa hukumar ta samu rahoton cewa matar ta gudu zuwa Jihar Zamfara, amma ana ci gaba da ƙoƙarin dawo da ita zuwa Kano domin ta fuskanci shari’a tare da Mai Wushirya.