Kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a kofar fada a Hadejia karkashin mai shari’a, Aliyu Muhammad Kwalam ta raba wani aure da aka yi ba bisa ka’ida ba.Â
Wadanda ake tuhumar su biyar, sun hada da ango da amarya da waliyyansu da kuma mai masaukin baki.
- Malamar Jami’ar Nasarawa Da Aka Sace Ta Kubuta
- Karbar Haraji Mai Yawa Ne Ya Durkusar Da Masana’antu A Nijeriya – Kwamiti
Dansanda mai gabatar da kara, Sufeto Yau Ismail ya ce ana tuhumarsu da aikata laifuka uku da suka hada hadin baki da tada hankalin jama’a laifin da ya saba wa sashen doka ta 122.
Wadanda ake karar sun hada ango Yahya Isah da amarya Sa’adatu Rabi’u da kuma wakilin ango Yakubu Yakson da waliyyin amarya Usman Rabi’u, da kuma Adamu Abdullahi da ke zama babban shaida kuma mai masaukin baki.
Wadanda ake tuhumar sun amsa laifukansu dalilin da ya sa kotun ta aike da su zuwa gidan ajiya da gyaran hali zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba, 2023 don ci gaba da saurarar karar.