Kwamitin shugaban kasa kan inganta karbar haraji da dokokin kudi ya shawarci gwamnatin Nijeriya da ta zabtare wasu jerin haraji har 190 da ake karba daga hannun talakawan kasar nan.
Wannan dai ta zama wata hanya da za a bi wajen sakarwa masu kamfanonin da masana’antu mara, ta yadda za su samu damar gudanar da ayyukansu da kuma samun riba cikin sauki.
- Kotun Koli Ta Tsayar Da Ranar Alhamis Don Yanke Hukunci Kan Zaben Shugaban Kasa
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Fika Ya Rasu Yana Da Shekara 90
A cikin wani rahoto bayan bincike da kwamitin ya gabatar wa shugaba Tinubu, ya zargi jihohi da karbar harajin da ya wuce kima, kuma bisa rashin ka’ida.
Rahoton kwamitin ya ce wannan harajin barkatai da jihohi ke karba, shi ne sanadin tashin farashin kayayyaki da rashin samun ribar da ta dace da kuma lalacewar darajar Naira da sauran matsaloli.
Kwamitin ya yi misali da korafin da kamfanonin sadarwa suka jima suna yi game da yadda jihohi suka mayar da su saniyar tatsa ta yadda suke karbar jerin haraji.
Yayin da yake gabatar da korafin kamfanonin sadarwar, shugaban kungiyar kamfanonin, Gbolahan Awonuga ya ce kowanne kamfanin sadarwa yana biyan haraji daban-daban har guda 40 ko sama da haka duk wata, abin da ya ce yana haddasa musu karancin abokan ciniki saboda tsada.
Shugaban kwamitin shugaban kasa Mista Taiwo Oyedele ya ce kwamitin na shawartar gwamnatin tarayya ta hade haraji fiye da 200 daban-daban da masu kamfanoni ke biya zuwa 10.
Kwamitin ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta yi gaggawar mayar da hankalin kan fannin tattalin arziki, don shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki da kuma lalacewar darajar Naira.
Ana ci gaba da kokawa kan yadda farashin kayan masarufi ke yin tashin gwauron zabi, lamarin da ya sanya dubban mutane gaza cin abinci sau uku a rana.