Kotun shari’ar addinin Musulunci da ke zamanta a hukumar hisbah ta jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Malam Sani Tamim Sani Hausawa, ta yanke wa ‘yar TikTok, Ramlat Muhammad, hukuncin daurin watanni 7 a gidan gyaran hali.
Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata LEADERSHIP HAUSA ta rawaito muku cewa Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta gurfanar da matashiyar a gaban kotu, kan wasu kalamai da ta yi na cewa ita ‘yar madigo ce kuma duk namijin da zai aureta sai ita ma ta auro tata matar.
- NAF Ta Kama Shahararren Mai Garkuwa Da Mutane A Karamar Hukumar Takai A Jihar Kano
- Zargin Baɗala: Kotu Ta Umarci A Binciki Lafiyar Ƙwaƙwalwar Murja Kunya
Mai Shari’a Malam Sani Tamim, ya ce, kotun ta sami Ramlat Muhammad wadda ake wa lakabi da Princess da laifin badala da fitsara da kuma yawon banza.
Mai Shari’a Sani Tanimu Hausawa ya yanke wa Ramlat hukuncin dauri na tsawon watanni bakwai ko zabin biyan tarar Naira 50,000.
A tuhumar farko Alkalin ya yanke wa Ramlat hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata uku ko zabin tara ta Naira dubu talatin. Sai laifin yawon banza, wanda a kansa alkalin ya yanke mata hukuncin daurin wata uku ko zabin tara na Naira 20,000.
A laifi na uku da aka kama ta da shi na fitsara kuma alkalin ya yanke mata hukunci bisa sassauci da ta nema na zaman gidan yari na tsawon wata daya babu zabin tara.