Babbar Kotun Abuja, ta sauya sharuddan belin da ta ba tsohon gwamnan babban banki (CBN), Godwin Emefiele, inda a yanzu ta bashi damar yin tafiye-tafiye a cikin Nijeriya.
A watan Nuwamban 2023 ne, kotun ta bada belin Emefiele kan kudi naira miliyan 300,000000, sannan dukkanin wadanda za su tsaya masa su kasance sun mallaki fili na kwatan-kwacin wannan kudi a yankin da kotun ke da hurumi kuma su mika su ga kotun.
- AFCON 2023: Mun Shirya Fafatawa Da Ivory Coast – Ibrahim Gusau
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Yaba Da Abota Da Goyon Bayan Juna Da Togo
Haka nan mai shari’a Hamza Muazu, a lokacin bada belin, ya umarci Emefiele da ya mika fasfo dinsa, sannan kuma ya kasance a Abuja har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.
Sai dai a zaman kotun na yau Alhamis, lauyan Emefiele, Matthew Burkaa ya shaida wa kotun cewa wanda yake karewa ya shigar da wata bukata a ranar 10 ga watan Janairu 2024, inda yake neman kotun ta sauya sharudan belinsa don ba shi damar barin Abuja zuwa wasu sassa na kasar nan.
Lauyan mai shigar da kara, Rotimi Oyedepo, bai yi suka kan bukatar ba, sai dai ya bukaci kotun da ta tabbatar da cewa wanda ake kara bai fice daga kasar ba a yayin shari’ar da ake tuhumarsa.
A hukuncin da mai shari’a Muazu ya yanke kan wannan bukata, ya bai wa Emefiele damar yin balaguro cikin kasar nan har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.