Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin, DCP Abba Kyari, na tsawon makonni biyu bayan ya shafe tsawon watanni 27 a tsare.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Kyari ya rasa mahaifiyarsa, Mama Yachilla Kyari, a farkon wannan watan wannan wata lokacin da yake tsare.
- Kotu Ta Tsare Wani Mutum Kan Zargin Kashe Wani Tsoho Ɗan Shekara 70
- Liƙi Da Takardun Naira Ya Jefa Wata Mata Komar EFCC A Gombe
Daga nan ne kotun ta sanya ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu, domin tantance bukatar neman belinsa a shari’ar da ake yi masa kan tuhume-tuhumen da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta shigar, biyo bayan kama shi da aka yi sama da shekaru biyu, wato a ranar 14 ga watan Fabrairu, 2022.
Idan za a tuna mahaifiyar Kyari ta rasu ne da sanyin safiyar Lahadi, 5 ga Mayu, 2024, kuma ta bar ‘ya’ya 10 ciki har da Abba Kyari, wanda shi ne babban ɗa a wajenta.