BBC ta rawaito cewa, wata Kotu da ke zamanta a birnin Makurdi ta bai wa, Dokta Iyorchia Ayu, umarnin daina nuna kansa a matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP a Nijeriya.
AlÆ™ali Wilfred Kpochi wanda ya bayar da umarnin, ya buÆ™aci Ayu ya janye daga shugabancin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a saurari Æ™arar da tuni aka shigar.
- PDP Ta Dakatar Da Shugabanta Na Kasa Kan Zargin Yi Wa Jam’iyyar Adawa Aiki
- Zaben Gwamna: PDP Za Ta Yi Zanga-Zangar Kwana 7 Kan Sakamakon Zaben NasarawaÂ
Tun farko, ƙarar da Injiniya Conrad Utaan ya shigar ta nemi kotu ta hana Ayu daga bayyana kansa a matsayin shugaban PDP kasancewar dakatarwar da aka yi masa.
PDP ta dakatar da Ayu NE bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amanar jam’iyyar.
Shugabannin jam’iyyar a matakin gundumarsa da ke Æ™aramar hukumar Gboko, a jihar Benue ne suka É—auki matakin.
Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kaÉ—a Æ™uri’ar rashin Æ™warin gwiwa kan ayyukansa.