BBC ta rawaito cewa, wata Kotu da ke zamanta a birnin Makurdi ta bai wa, Dokta Iyorchia Ayu, umarnin daina nuna kansa a matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP a Nijeriya.
Alƙali Wilfred Kpochi wanda ya bayar da umarnin, ya buƙaci Ayu ya janye daga shugabancin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da tuni aka shigar.
- PDP Ta Dakatar Da Shugabanta Na Kasa Kan Zargin Yi Wa Jam’iyyar Adawa Aiki
- Zaben Gwamna: PDP Za Ta Yi Zanga-Zangar Kwana 7 Kan Sakamakon Zaben Nasarawa
Tun farko, ƙarar da Injiniya Conrad Utaan ya shigar ta nemi kotu ta hana Ayu daga bayyana kansa a matsayin shugaban PDP kasancewar dakatarwar da aka yi masa.
PDP ta dakatar da Ayu NE bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amanar jam’iyyar.
Shugabannin jam’iyyar a matakin gundumarsa da ke ƙaramar hukumar Gboko, a jihar Benue ne suka ɗauki matakin.
Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kaɗa ƙuri’ar rashin ƙwarin gwiwa kan ayyukansa.