Babbar Kotun Jihar Kano ‘, ta ƙi amincewa da buƙatar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, na son hana ci gaba da shari’ar da ake yi a kansa kan zargin cin hanci da rashawa.
Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta yanke hukuncin cewa kotun na da hurumin sauraron shari’ar.
- Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi
- Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe
Ta ce ƙorafin da lauyoyin Ganduje suka shigar ba su da ƙarfi.
Ta tabbatar da cewa ƙarar da gwamnatin Jihar Kano ta shigar na kan ƙa’ida kuma kotu za ta ci gaba sauraron shari’ar.
Ana tuhumar Ganduje da matarsa, Hafsat Umar, da wasu mutane shida da aikata laifuka 11 da suka shafi cin hanci da rashawa.
Waɗanda ake tuhuma sun haɗa da zargin cin hanci, haɗa baki, da karkatar da kuɗin jama’a da yawansu ya kai biliyoyin Naira.
Sauran waɗanda ake zargi sun haɗa da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad da wasu kamfanoni uku; Lamash Properties Ltd., Safari Textiles Ltd., da Lasage General Enterprises Ltd.
Alƙalin ta ce an shigar da ƙarar yadda ya dace kuma dole a ci gaba da shari’ar.
Ta kuma ce za a ci gaba da shari’ar ko da Ganduje da sauran mutum shida da ake tuhuma ba su halarci zaman kotun ba.
An aike wa Lamash Properties Ltd., ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma sammaci.
Tun da farko, lauyar matar Ganduje, Misis Lydia Oyewo, ta roƙi kotu da ta soke ƙarar tana mai cewa ba ta da hurumin sauraren shari’ar.
Sauran lauyoyin da ke kare ragowar waɗanda ake tuhuma sun shigar da irin wannan buƙata.
Amma lauyan gwamnati, Adeola Adedipe (SAN), ya ce waɗannan ƙorafe-ƙorafe ba su da tushe.
Ya roƙi kotu da ta ci gaba da sauraron shari’ar domin a tabbatar da adalci.
An ɗage shari’ar zuwa ranakun 30 da 31 ga watan Yuli, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp