Kotu ta dage sauraron kara da hukumar kasuwar Abubakar Rimi ta shigar akan yan kasuwar Sabon Gari zuwa karshen shekara.
Lauyan ‘yan Kasuwar ta Sabon Gari, Batista Abdul’aziz Adam Muhammad ya ce asalin kararsu dake gaban kotu shine matsayin rumfuna da yan kasuwar suka gina bayan gobara da akayi a kasuwar Sabon gari da haraje-haraje da ake kallafa musu mara tsari.
Saboda haka su yan kasuwa sukace tunda babban kotu ta riga tayi hukunci ,kotun ba tada hurumin sauraran wani abu dake gaban kotun koli.Bayan sun zo da wannan suka, shine kotun ta daga sauraran karar zuwa 12/12/2022 dan cigaba da saurara.
Lauyan yan kasuwar ya ce duk wani hakki na hukuma ba abinda yan kasuwar basu biya ba, abinda doka ta tanada a biya, sunje zasu biya akace karsu biya sai an yiwa dokar gyara, akazo aka gyara dokar sukace zasu biya, amma shugaban hukumar kasuwar ya ce bazai karba ba, har sai an koma an gyara dokar daidai da son ransa ba yanda zai amfani yan kasuwar ba, shi ne sukace a bari sai abinda kotu tace.
Batista Abdul’aziz Adam Muhammad ya ce suna da yakini kotu za tayi musu adalci, saboda a kotun kasa anyi abinda sukayi godiya kuma da aka daukaka kara anyi abinda suka yi godiya duk sukace basu yarda ba, suka tafi kotun koli suna jira aje za su je duk inda suka je, abin da fatansu kotu ta yi duk abinda yake na adalci duk abinda aka yi hukunci na adalci a shirye suke su gayawa yan kasuwar su karbi hukuncin su yi biyayya ga doka.
Shima lauyan hukumar kasuwar Abubakar Rimi Batista Abdullahi ya ce sun zo kotu, amma bata iya sauraran shari’ar yadda yakamata ba, saboda wanda ake kara dasu, basu iya maido da takardunsu na martani akan lokaci ba, suna da bukatar lokaci da zasu mayar musu da martani ba.
Dinbin ‘yan kasuwar Muhammad Abubakar Rimi dana Singa suka ajiye harkokinsu suka hallara a kotun a safiyar ranar Talata don jin yadda shari’ar za ta kaya.