Wata babbar kotun shari’a Musulunci da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, ta dage ci gaba da sauraron karar da aka shigar kan wani mutum da ake zargi da auren jikansa.
Alkalin kotun, Malam Bashir Mahe, ya dage ci gaba da sauraren karar domin bai wa lauyan wanda ake kara, Abubakar Ayuba, damar yin nazari kan tuhume-tuhumen da ake yi wa wanda yake karewa.
- Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukuncin Sharar Titi Da Bulala 12 A Kano
- Ban Taba Goyon Bayan Tinubu Don Ya Zabe Ni A Matsayin Mataimakinsa Ba – Shettima
Hukumar Hisbah ce ta shigar da karar, inda take neman a warware auren da aka daura shekara 20 da ta gabata.
Hisbah ta shaida wa kotun cewa, auren da aka yi tsakanin Malam Musa Dangote da Wasila Musa ‘yar yayansa, ya saba wa dokokin shari’a da kuma tsarin shari’ar Musulunci.
Hukumar ta ce ta shigar da kara a kan ma’auratan ne bayan kokarin da Majalisar Shawarar Malaman addinin musulunci (Shura) da Masarautar Tsafe suka yi na ganin abun bai je kotu ba abi maslahar abun ya ci tura, inda magidanci ya ce ba za ta sabu bindiga a ruwa ba.
Lauyan hukumar Malam Sani Muhammad, ya shaida wa kotun cewa binciken da hukumomin addinin musulunci daban-daban da masarautar suka yi ya nuna cewa ma’auratan da suka yi aure a 1999 suna da alaka kai tsaye ta jini don haka ya haramta aure a tsakaninsu.
Muhammad ya ce, matakin ya saba wa koyarwar addanin Musulunci kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani sura uku aya ta 23.
Don haka ya roki kotu da ta gaggauta yanke auren.
A halin da ake ciki, Ayuba, ya musanta zarge-zargen kuma ya bukaci samun damar bin rahoton binciken hukumar da ta gabatar a matsayin shaida.
Ayuba ya kuma bukaci a ba shi lokaci domin nazarin tuhumar da kuma shirya kariya.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin mika rahoton binciken hukumar ga lauyan da ke kare wadanda ake kara sannan, ya ba shi kwanaki biyar ya yi nazari tare da bayar da amsa gamsasa a gaban kotu.
Daga nan ne alkalin ya dage zaman domin ci gaba da sauraren karar zuwa ranar Litinin mai zuwa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa Musa mai shekaru 35 ya haifi ‘ya’ya takwas a cikin auren shekara 20 da suka yi, don yanzu haka ake neman warware shi.