Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC kan amsar kudin fom na tsayawa takarar shugaban Karamar hukuma akan Naira miliyan 10 da kuma naira miliyan 5 ga ‘yan takarar kansiloli a zaben da ke tafe a jihar.
Hukuncin, wanda mai shari’a Emeka Nwite ya zartar a ranar Larabar da ta gabata ya biyo bayan wani kudiri da jam’iyyun APP, da ADP, da SDP suka shigar gabanta.
- An Zartas Da Sanarwar Beijing Da Tsarin Aiki A Taron FOCAC
- Nijeriya Ta Zama Kasa Ta 3 Da Ta Fi Karbar Bashin Bankin Duniya
Masu shigar da karar dai, sun yi zargin cewa, ba a yi adalci ba kuma an take hakkokin dimokuradiyya wajen kayyade kudaden fom din neman mukaman na siyasa.
Wannan hukuncin da kotun ta yanke, ya biyo bayan sanarwar da Shugaban Hukumar KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, ya yi a ranar 15 ga watan Agusta, 2024, cewa, an bukaci masu neman tsayawa takarar kujerar kananan hukumomi su biya Naira miliyan 10 da kuma Naira miliyan 5 ga wadanda ke neman kujerar kansila.
Hukuncin kotun ya dakatar da aiwatar da wadannan kudiri har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron karar wacce aka dage zuwa ranar 25 ga Satumba, 2024.
KANSIEC ba ta mayar da martani kan wannan hukuncin ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton kan yadda wannan umarni zai shafi zaben kananan hukumomin da za a yi a ranar 26 ga Oktoba, 2024.