Wata babbar kotun jihar Kano ta hana gwamnatin tarayya yin katsalandan ga kudaden kananan hukumomi 44 da ke jihar.
Mai shari’a Musa Ibrahim Karaye ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, biyo bayan karar da wakilan kananan hukumomin jihar suka kai na kare ‘yancinsu na cin gashin kansu ga kudaden da gwamnatin tarayya ke ware musu.
- Shugaba Xi Ya Halarci Taron Kamfanoni Masu Zaman Kansu Tare Da Gabatar Da Jawabi
- An kwato Murafun Kwalabati 125 Da Aka Sace A Abuja
Rikicin shari’ar ya samo asali ne bayan da jam’iyyar adawa ta APC ta nemi kotu da ta bayar da umarnin dakatar da bai wa kananan hukumomin jihar kudaden gashin kansu, bisa zargin tafka magudi a zaben kananan hukumomin da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ta gudanar a watan Oktoban 2024.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Hon. Abdullahi Abbas, Hon. Aminu Aliyu Tiga, da Jam’iyyar APC ne suka shigar da karar inda suke kalubalantar wasu hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi da suka hada da Babban Bankin Nijeriya (CBN), Asusun raba kudi na Tarayya (FAAC), da kuma dukkan kananan hukumomi 44 da ke Kano a gaban kotu.
Sai dai kuma hukuncin da babbar kotun Kano ta yanke ya tabbatar da hakkin kananan hukumomi na samun kudadensu, tare da hana gwamnatin tarayya ko wasu hukumominta rike kason su.
Da yake jawabi bayan yanke hukuncin, lauyan kananan hukumomi 44, Barista Bashir Wuzirchi, ya bayyana matakin a matsayin nasara ga jihar Kano.