Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar, Xi Jinping ya halarci wani taron tattaunawa na kamfanoni masu zaman kansu a yau Litinin.
Xi, wanda har ila yau shi ne shugaban kwamitin tsakiya na sojin kasar, ya gabatar da muhimmin jawabi bayan sauraron ra’ayoyin wakilan ‘yan kasuwa masu zaman kansu.
Li Qiang, firaministan kasar Sin, da Ding Xuexiang, mataimakin firaministan kasar, su ma duk sun halarci taron, wanda Wang Huning, shugaban majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, ya jagoranta. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp