Wata babbar kotun jihar Ribas da ke yankin Isiokpo a karamar hukumar Ikwerre ta jihar, ta bayar da umarnin wucin gadi na hana majalisar dokokin jihar da kakakin majalisar, Martin Amaewhule aiwatar da duk wani mataki da ya shafi tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.
Gwamna Sim Fubara ya shigar da karar ne ta hannun lauyansa, Damian Okoro (SAN), a safiyar ranar Laraba.
- Dankwambo Ya Ce Daga Yanzu Gwamnatin Gombe Ta Daina Biyansa Fansho Ya Yafe
- Hausawa ‘Yan Kasuwar Shanu Na Neman Sasantawa Da Gwamnatin Abiya
Mataimakin kakakin majalisar, Dumle Maol, magatakarda na majalisar da kuma babban alkalin jihar, Mai shari’a Simeon Chibuzor Amadi, su ma an hana su.
Alkalin kotun, Mai shari’a Ben Whyte ya bayar da wannan umarni ne biyo bayan karar da aka shigar a kan wadanda ake kara kuma ya umarci bangarorin su dakata har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan kudirin da aka gabatar kan sauraron karar zuwa ranar 14 ga Nuwamba, 2023 don gabatar da karar.
Tun da fari rikicin siyasa ya kunno kai tsakanin gwamnan jihar mai ci da uban gidansa, Nyesom Wike.
Sai dai gwamnonin jam’iyyar PDP sun ziyarci ministan na babban birnin tarayya don yin sulhu, inda Wike ya jinjina musu kan ganin an zauna lafiya.
Shi ma Shugaba Tinubu ya gana da Fubara da Wike don ganin ya musu sulhu kan rikicin da ya kunno kai.