Wata babbar kotu a Jihar Legas, ta yanke wa wani basaraken Shangisha da ke karamar hukumar Alimosho, Michael Matiu Yusuf, hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari saboda samunsa da laifin yin garkuwa da kansa.
Kotun dai ta yanke masa hukuncin ne tare da wani mai suna Adams Opeyemi Mohammed, wanda ya taimaka masa wajen aikata damfarar, yayin da kuma aka sallami matarsa Abolanle.
- Gobara Ta Lalata Gidaje 80 A Sri Lanka – ‘Yansanda
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Babban Da Ga Dan Majalisar Dokokin Bauchi
Mai shari’a Hakeem Oshodi, ya ce an yanke musu hukunci ne don ya zama izina ga wasu.
Tunda farko dai, mai gabatar da kara ya ce a ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2017 ne, basaraken ya yi garkuwa da kansa da zummar haifar da rashin zaman lafiya, lamarin da ya ce ya saba wa sashe na 5 da ya haramta garkuwa da mutane na Jihar Legas a shekarar 2017.
Tuni dai gwamnatin jihar a wancan lokacin karkashin Akinwunmi Ambode ta dakatar da basaraken daga matsayinsa, tun bayan da ‘yansanda suka kama shi tare da Mohammed, kamar yadda sashe na 38 (1) na dokar masarautun Jihar Legas ta tanadar.