Wata kotun majistire da ke Jihar Bauchi, karkashin jagorancin Haruna Abdulmumini Mamman ta daure wani matashi dan shekara 32 a duniya, Auwal Usman a gidan yari na tsawon shekara biyu bisa samunsa da laifin sare hannayen abokinsa da adda sakamakon rigimar da ta barke a tsakaninsu.
Tun da farko dai, dan sanda mai shigar da kara, Yusuf Musa ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargi, Auwal Usman mazaunin kauyen Ari da ke karamar hukumar Ningi, biyo bayan rashin jituwa tsakaninsa da Sabo Abduwa, wanda hakan ta sanya su bai wa hammata iska.
- Bidiyon Dala: Gwamnatin Kano Ta Fara Bincike Akan Ganduje
- Jihohi 14 Da Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa —NEMA
Hakan ya sa Auwal dauko adda tare da sare hannun abokinsa guda biyu.
Musa ya kara da cewa, an dauki Abduwa zuwa babban asibitin Ningi yayin da ake yanke dayan hannun domin ceton rayuwarsa sakamakon munanan raunuka da ya samu.
A cewar dan sandan wannan ya saba wa sashe na 241 na kundin final kod.
Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa, sai dai ya roki sassauci a wajen kotun kan cewar wannan shi ne laifi ma farko da ya taba aikatawa.
A hukuncinsa da ya yanke a jiya, alkalin kotun magistraten, Haruna Abdulmumini Mamman, ya ce wanda tsautsayin ya rutsa da shi, ya rasa hannayensa biyu sakamakon mummunan aika-aikar wanda ake zargi.
Don haka ya yanke wa wanda ake zargi zaman gidan gyara hali na tsawon shekara biyu ba tare da tara ba.
Sannan, ya umarce sa da ya biya Naira 150,000 kudin jinya ga wanda lamarin ya shafa.