Wata Kotun Majistare ta 3 da ke zama a Yola, Jihar Adamawa, a ranar Litinin, ta bayar da umarnin a tsare wasu mutane 3 a gidan yari bisa zargin kashe wani mai suna Thomas Godwin Zamfara.
Wadanda ake tuhuma da suka hada da Godwin Chaakukuyada da Ibrahim Bakari da Danlami Ali an gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin kashe marigayi Zamfara yayin da kuma ake kan neman wani da ake zargi mai suna Stephen Peter.
- Xi Jinping Ya Ba Da Umurni Game Da Babban Shirin Shekaru Biyar-Biyar Na Bunkasa Tattalin Arziki Da Zamantakewar Kasar Sin Na 15
- Abin Da Ya Dace Ki Yi Yayin Haila Da Bayan Kin Gama?
A cewar rahoton farko da aka gabatar a gaban kotu, an kashe marigayin ne yayin da ya ke kan hanyarsa daga Fadamar Rake zuwa Kala’a inda ya gamu da munanan hare-haren ‘yan bangar siyasa da ake zargin wani fitaccen dan siyasa ne ya turo su.
Wadanda ake tuhumar dai, a cewar rahoton farko, sun yi wa mamacin dukan tsiya har sai da ya suma, inda aka garzaya da shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya ta Hong inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Dukkan wadanda ake tuhumar dai sun ki amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen.
Kotun da ke karkashin Alkali Uwani Danladi, ta bayar da umarnin a garkame wadanda ake kara a gidan gyaran hali don bai wa ‘yansanda damar kammala bincike tun da har yanzu akwai sauran mutum daya da ake tuhuma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp