Wata babbar kotu a jihar Kano ta bayar da sanarwar dakatar da Sufeto Janar na ‘yan sanda da Mataimakin Sufeto Janar na shiyyar ta 1 Kano, da kwamishinan ‘yansandan Kano daga gayyata ko kama shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa.
Idan za a iya tunawa LEADERSHIP HAUSA ta rawaito muku cewa wasu da suka kira kansu shugabannin jam’iyyar APC a matsabar Ganduje sun dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, wanda jam’iyyar a matakin jihar ta soke takatarwar.
Tun daga nan ne ‘yan jam’iyyar a matsabar suka dauki matakin shari’a, inda suka nemi kotu ta tabbatar da dakatarwar da suka yi wa Ganduje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp