Babbar Kotun Tarayya da ke birnin tarayya, Abuja ta haramta wa tsohuwar Ministar Mata da Walwalar Al’umma, Pauline Tallen sake rike wani mukamin gwamnati.
A wani hukunci da ta yanke a ranar Litinin, kotun ta yi tir da kalaman da tsohuwar ministar da ta yi a shekarar da ta wuce, inda ta caccaki wani hukuncin kotun tarayya da ke Jihar Adamawa.
- Sanata Barau Jabril Na Kokarin Hana Shoprite Tashi Daga Kano
- Wakilin Sin Na Musamman Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Madagascar
Kotun da ke zamanta a birnin Yola, babban birnin Adamawa, ta soke cancantar takarar A’ishatu Dahiru Binani ta jam’iyyar APC da ke neman kujerar gwamnan jihar.
Sai dai Tallen ta nuna rashin gamsuwarta da hukuncin na kotun wanda ta bayyana a matsayin “musgunawa wani bangare na al’umma”, yayin da ta bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da hukuncin.
Shugaban lauyoyi na kasa, Yakubu Maikyau ya bukaci Tallen da ta nemi afuwa kan kalamanta, inda har ya yi barazanar maka ta a gaban kuliya.
Sai dai tsohuwar ministar ba ta nuna halin ko-in-kula ba, abin da ya sa kungiyar lauyoyin ta maka ta a gaban kotu.