Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’a a a ranar Litinin kan wani kudiri da ke bukatar Isra’ila da Hamas su tsagaita bude wuta don samun damar shigar da kayayyakin agaji cikin Zirin Gaza ta kan iyakokin kasa da ruwa da kuma ta sama.
Jami’an diflomasiya sun ce, makomar wannan kudirin da aka shata a Kwamitin Tsaron na Majalisar Dinkin Duniya na fuskatar barazana, duba da cewa a baya, Amuka ta yi amfani da karfin kujerarta wajen dakile cimma jituwar.
- Kotu Ta Haramta Wa Tsohuwar Minista Rike Mukami A Nijeriya
- Muhimmancin Manufofin Sin Wajen Ingiza Ci Gaban Duniya
Duk wani kudiri dai na Kwamitin Tsaron na bukatar akalla kuri’un kasashe tara ba tare da samun wata kasar da ta hau kujerar na ki ba daga cikin kasahen Amurka da Faransa da China da Birtaniya da kuma Rasha kafin amincewa da shi.
A bangare guda, a wannan makon ne ake sa ran Ministar Harkokin Wajen Faransa, Catherine Colonna za ta isa Lebanon duk dai don tattaunawa kan batun tsagaita bude a kan iyakar Isra’ila.
Uwargida Catherine za ta gana da Firaministan Lebanon Najib Mikati da kuma kakakin majalisar dokokin kasar, Nabih Berri, wanda babban amini ne ga kungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da ragargazar Gaza duk kuwa da caccakar da masu rajin kare hakkokin bil Adama adama ke yi wa kasar na cewa, da gangan ta ke jefa Falasdinawa cikin yunwa da sunan yaki.