• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Ki Bayar Da Belin Wanda Ya Yi Sanadin Rasa Kafar Fatima

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
3 years ago
Kotu

Babban lauuyan gwamnatin Jihar Sakkwato kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Sulaiman Usman (SAN), ya karbi ragamar gudanar da shari’ar da aka shigar a na karar Aliyu Sanusi Umar wanda ya kade daliba Fatima Sulaiman ‘yar shekaru 16 wanda hakan ya zama silar yanke mata kafa. 

An gurfanar da Umar ne a gaban Babbar Kotun Majistare da ke Arkilla a bisa ga tukin ganganci, tuki ba tare da lasisi ba tare da yi wa Fatima babbar illa a gaban makarantusu bayan ta kammala rubuta jarabawar karshe.

  • ‘Yan Ta’adda Sun Tarwatsa Kauyuka 21 A Sakkwato
  • An Gano Ayyukan Kutsen Yanar Gizo Da NSA Ta Amurka Ta Yi Wa Wata Jami’ar Kasar Sin

A zaman kotun a jiya, Babban Lauyan Gwamnati, a baki ya bukaci kotun da ta ba shi damar karbar shari’ar bisa ga dogaro da sashe na 211 na tsarin mulkin Kasa na 1999 da kuma sashe na 106 na Kundin dokar shari’a ta Jihar Sakkwato.

Babban Lauyan Gwamnatin wanda ya samu wakilcin Barista Sufyanu Umar Mai- Kulki ya bayyana cewar kundin dokokin da ya gabatar, sun bashi damar karbar ragamar duk wata shari’ar miyagun laifuka wadda wani ko wata Hukuma ta shigar.

Haka ma Lauyan ya bukaci kotun da ta dage sauraren shari’ar zuwa mako daya domin ba shi damar shiryawa shari’ar yadda ya kamata.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Sai dai Lauyan mai kariya, Jacob Ochidi (SAN) ya nuna rashin aminta da bukatar karbar shari’ar a baki yana cewar tun farko kotu ta aminta da gudanar da sauri a shari’ar daga ranar Talata. Ya ce idan har ba za a gaggauta shari’ar ba, to a bayar da belin wanda yake kariya domin a cewarsa ga alamu za a tsawaita shari’ar.

Da take yanke hukunci kan matsayar kotu, Mariya Haruna Dogon-Daji ta sa kafa ta yi fatali da bukatar bayar da wanda ke kariya beli ta na cewar an yi sauri idan aka bayar da belinsa a wannan lokacin. A kan wannan ta dage zaman kotun zuwa ranar 19 ga Satumba tare da bayar da umurnin ci-gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan gyara hali.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka
Kiwon Lafiya

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu
Manyan Labarai

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Next Post
Dubban Mutane Sun Yi Zanga-Zangar Adawa Da Mulkin Soji A Sudan

Dubban Mutane Sun Yi Zanga-Zangar Adawa Da Mulkin Soji A Sudan

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

October 25, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

October 25, 2025
Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.