Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar Naira biliyan ɗaya da wani lauya daga Abuja, Uthman Isa Tochukwu, ya shigar kan tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, da wasu.
Mai shari’a Inyang Ekwo ne, ya kori ƙarar saboda wanda ya shigar da ita bai halarci kotun ba, kuma bai aike da lauya da zai wakilce shi ba.
Alƙalin ya ce ya tabbatar da cewa wanda ya shigar da ƙarar ya yi watsi da shari’ar saboda ƙin bayyana a kotu ba tare da wata hujja ba.
An shigar da ƙarar tun shekarar 2023, inda mai ƙarar ke zargin Buhari, Antoni Janar, Babban Bankin Nijeriya da wasu bankuna biyu da jefa mutane cikin wahala biyo bayan sauya fasalin takardun Naira.
Mai ƙarar ya nemi kotu ta umarce su da biya sa diyyar Naira biliyan ɗaya saboda keta masa ‘yancinsa.
Haka kuma ya nemi kotu da ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da kuma 1000.
Baya ga haka, ya buƙaci a umarci su da su nemi gafara ta hanyar wallafa bayani a manyan jaridu biyu na ƙasa.
Amma a zaman kotu na ranar Litinin, wanda ya shigar da ƙarar da lauyansa ba su halarci zaman kotu ba.
Lauyan da ke kare Emefiele da CBN, Mista Chikelue Amasiani, ya sanar da kotu cewa tun da aka shigar da ƙarar, mai ƙarar da lauyansa ba su nuna wata alama ta son ci gaba da shari’ar ba.
Ya roƙi kotun da ta kori ƙarar.
Mai shari’a Ekwo ya amince da buƙatar kuma ya kori ƙarar, inda ya bayyana cewa mai ƙarar zai iya dawo da ita idan ya shirya yin shari’ar da gaske.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp