Kotun Daukaka Kara da ke Birnin Tarayya Abuja ta tabbatar da Hukuncin Kotun Sauraren Zaben Kano da ya tabbatar da nasarar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a ranar Juma’a.
Tun da farko Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya shigar da kara gaban Kotun yana kalubantar ayyana Nasiru Gawuna na APC da Karamar kotun zabe ta tabbatar da nasararsa.
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kori Gwamna Abba Gida-Gida Ta Tabbatar Da Nasarar Gawuna
- NNPP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamnan Kano Da Ta Ba Gawuna Nasara
Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce, Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta yi daidai da ta ce, Abba Kabir Yusuf, ba ɗan jam’iyyar NNPP bane. Kotun ta ce, Wajibi ne sai mutum ya zama dan jam’iyya kafin ya samu cancantar tsayawa takara a Nijeriya.
Kotun ta ce, Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta na da hurumin shiga abinda ya shafi harkokin jam’iyya, kuma ta ce, duk da Dr. Nasiru Gawuna, ba ya cikin masu shigar da kara, zai iya amfana da hukuncin kotu idan aka tabbatar da cancantarsa.
Kazalika, Kotun Ɗaukaka Karar ta ce, hukuncin da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta yanke ta Manhajar Zoom ta yi daidai.
Kazalika, Kotun ta ci tarar Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar NNPP tarar naira miliyan daya (1,000,000) saboda bata wa kotu lokaci da suka yi.