Babbar kotun jiha mai lamba 5 dake zamanta a Kano ta saka ranar 28 ga watan Yuli na wannan shekarar domin yanke hukuncin karshe akan zargin da ake yiwa Abdulmalik Tanko na kashe dalibar makarantar sa, Hanifa Abubakar.
An zargi Abdulmalik Tanko ne dai da garkuwa da Hanifa tare da kashe ta, bayan ya hada baki da wasu mutane guda biyu, Hashim Isiyaku da Fatima Musa, wadda ake zargin budurwar sa ce.
A ranar 20 ga watan Janairun wannan shekarar ne dai jami’an tsaro a Kano suka tono gawar Hanifa a wani rami dake cikin makaranta, bayan an kashe ta.
A yayin zaman da akayi a Kwanakin baya, Abdulmalik Tanko, wanda shine shugaban makarantar tare da wata Fatima Musa da Hashim Isiyaku suka bukaci a basu lauyan da zai dinga kare su.