Mai shari’a James Omotosho na babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya soke kasafin Naira biliyan 800 da Majalisar Dokokin Jihar Ribas, ta amince wanda Gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya gabatar.
Da yake yanke hukunci a Litinin, Mai Shari’a James Omotoso, ya ce kasafin da gwamnan ya gabatar a gaban mambobi hudu na majalisar da ke tsaginsa, haramtacce ne.
- Ba Irin Wannan Amurkar Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya Suke Bukata Ba
- Shugaban Kasar Sin Ya Ba Da Umarnin Ceton Mutanen Da Suka Bace A Zaftarewar Kasa Ta Kudu Maso Yammacin kasarÂ
Kotun ta kuma tabbatar da karar da majalisar da kakakin majalisar Martin Amaewhule suka shigar kan Fubara, wanda ya nemi a ba shi umarnin hana Gwamnan cikas a majalisar a karkashin jagorancinsa a matsayinsa na kakakin da sauransu.
Don haka ya umarci gwamnan ya sake gabatar da kasafin a gaban halastaccen zauren majalisar karkashin jagorancin Martin Amaewhule, daga tsagin tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.
Rikicin Wike da Fubara ya raba kan majalisar dokokin jihar, inda akasarin mambobin suke bangaren Wike sannan wasu suka sauya sheka zuwa APC.
A baya ‘yan majalisar sun tsige tsohon shugaban majalisar sannan suka nada daya daga cikinsu.
Gwamnan ya rike kudaden majalisar sannan ya sauya wa magatakardan majalisar da mataimakinsa wurin aiki, a matsayin martaninsa kan wadanda suka koma bangaren Wike.
Amma alkalin ya sanar cewa gwamnan ba shi da hurumin hana majalisar dokokin jihar kudadenta.
Daga nan ya yi wa gwamnan gargadi game da yunkurin kawo cikas ko yin katsa-landa ga harkokin gudanar da majalisar da Amaewhule ke jagoranta.
Alkalin ya kuma soke sauyin wurin aiki da gwamnan ya yi wa magatakardan majalisar da mataimakinsa.
Ya kuma umarci Sufeto-Janar na ‘yansanda ya ba da isasshen tsaro ga shugaban majalisar da mambobin majalisar da ke adawa da gwamnan.