Kotun sauraren kararrakin zaben ‘Yan Majlisar Tarayya a Sakkwato ta tabbatar da nasarar lashe zaben Honarabul Abdussamad Dasuki a matsayin dan majalisar wakilai a mazabar Kebbe/Tambuwal.
Kotun a yau Juma’a ta yi watsi da karar da Bala Kokani na jam’iyyar APC ya shigar a gaban ta a inda yake kalubalantar zaben Dasuki da jam’iyyarsa ta PDP tare da bukatar a bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara a zaben ko kuma a sake gudanar da zabe a wasu runfuna.
- Gwamnan Kano Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2024 Na Naira Biliyan 350Â
- Gwamnatin Kaduna Ta Mallaka Wa Rundujar Sojin Sama Fili Sama Da Hekta 43 Don Gina Gidaje
A hukuncin alkalan kotun uku da ta karanta a madadin masu shari’a Haruna Muhammad da Eke Eze, jagorar alkalan Josephine Oyefeso ta tabbatar da zaben Dasuki a matsayin halastacce da rinjayen kuri’u ba tare da sabawa dokokin zabe ba.
Kotun ta bayyana cewar masu karar sun kasa gabatar da gamsassun hujjojin magudin zabe da suka yi ikirari a cikin karar a zaben 25 ga Fabrairu wanda Dasuki ya samu kuri’a 47, 317 a yayin da Kokani ya samu kuri’a 34, 282.
Oyefeso ta bayyana cewar shaidu da hujjojin da masu kara suka gabatar ba amintattu ba ne da za su gurbata hukuncin Hukumar Zabe na ayyana Dasuki a matsayin wanda ya lashe zabe tare da cewar hakkin tabbatarwa yana a hannun Kokani wanda kuma ya kasa.
A kan hakan kotun ta yi watsi da karar tare da cin masu kara tarar naira dubu 250.