Wata kotun majistare a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wasu alkalan kotun shari’ar Musulunci takwas da ma’aikatan Hukumar Shari’a bakwai a gidan yari bisa zargin karkatar da kudin wasu marayu da ya kai Naira miliyan 99 a jihar.
Alkalin kotun Mai shari’a Mustapha Sa’ad Datti, ya bayar da wannan umarni ne a ranar Alhamis biyo bayan tuhumar karkatar da Naira miliyan 99 da hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC, ta shigar a gaban kotu kan mutane 15.
Alkalin kotun Mai shari’a Datti, ya bayar da umarnin a tsare wadanda ake kara a gidan yari har zuwa zaman kotun na gaba.
Wadanda ake tuhumar sun hada da Gazzali Wada, Yusuf Abdullahi, Sani Ali, Bashir Baffa, Sani Uba Ali, Hadi Tijjani Mu’azu, Mustafah Bala, da Alkasim Abdullahi.
Sauran wadanda ake tuhuma da ke tsare a gidan yari sun hada da Abdullahi Sulaiman Zango, Jaafar Ahmad, Bashir Ali Kurawa, Adamu Balarabe, Garba Yusuf, Aminu Abdulhadi, da Usaina Imam.
Kamar yadda aka gabatar, an tuhumi alkalan da ma’aikatan da wajen “hada baki, cin amana da kuma satar Naira miliyan 99.”
A halin da ake ciki, wadanda ake tuhumar duk sun musanta aikata laifin.
Don haka, babban lauyan wanda ya shigar da kara, Zaharaddin Kofar Mata, ya bukaci a dage zaman domin gabatar da kwararan shaidu a gaban kotun.
Biyo bayan bukatar da lauyan ya yi na a bada belin wadanda ake karar, kotun ta ki amincewa da bukatar da kuma bayar da umarnin a tsare wadanda ake karar a gidan yari.
An dage sauraren karar har zuwa ranar 1 ga watan Fabrairu, 2023 don ci gaba da sauraren karar.