Wata kotun majistare da ke zamanta a Ikeja ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai shekaru 42, Muyiwa Shonibare, bisa zarginsa da yin lalata tare da yi wa wata yarinya ‘yar shekaru 11 ciki.
Alkalin kotun, Misis E. Kubeinje, ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na Kirikiri.
- Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda A Borno Da Katsina
- Sojoji Sun Hallaka Kasurgumin Dan Bindiga, ‘Junaidu Fasagora’ Da Yaransa A Zamfara
Kubeinje ta umarci ‘yansanda da su aike fayil dinsa zuwa ofishin daraktan kararrakin jama’a (DPP) na jihar domin neman shawara.
Ta dage sauraron karar har zuwa ranar 24 ga watan Afrilu, 2024.
Rundunar ‘yansandan jihar, ta gurfanar da Shonibare da ke yankin Ikotun a Jihar Legas, kan laifin aikata lalata.
Mai gabatar da kara, SP Kehinde Ajayi, ya shaida wa kotun cewa Shonibare ya aikata laifin ne tsakanin watan Agusta zuwa Nuwamba, 2023.
Ya ce wata rana Shonibare ya yaudari yarinyar zuwa gidansa, inda ya yi lalata da ita har ta samu ciki.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya jeriya (NAN), ya ruwaito cewa laifin na iya jawo wa mutum daurin rai da rai karkashin sashe na 137 na dokar laifuka ta Jihar Legas, ta 2005.
Lalata da kananan yara na jawo hukuncin daurin shekaru bakwai, bisa ga tanadin sashe na 135 (1) (2) na dokar jihar.