ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Tura Alhassan Ado Dogwa Gidan Gyaran Hali

by Muhammad
3 years ago
Kotu

Wata kotun majisteri mai zamanta a Unguwar Normans land da ke Kano, ta tura Hon. Alhassan Ado Doguwa, gidan gyaran hali sakamakon zarginsa da harbe wasu mutane da kone su ranar Lahadin data gabata.

Ana zargin Alhassan Ado Dogwa, wanda shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Nijeriya da laifin harbi tare da kone mutane a karamar hukumarsa ta Tudun Wada da ke jihar Kano.

  • An Kama Alhassan Doguwa Kan Zargin Kisan Kai A Kano
  • An Kona Motoci Da Jikkata Wasu Yayin Artabu Tsakanin Magoya Bayan NNPP Da APC A Tudun Wada

Alkalin kotun mai lamba 54 ya ce, za a ci gaba da shari’ar Doguwan ranar 7 ga wannan watan da muke ciki.

ADVERTISEMENT

A yamma cin yau Laraba aka gurfanar da shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Nijeriya, Hon. Alhassan Ado Doguwa, bisa laifuka da suka hada da haɗin baki wajen aikata kisan kai.

Sauran laifukan da ake zarginsa da su sun haɗa da raunata mutane da dama tare da zargin hannu a kunna wuta a ofishin jam’iyyar hamayya ta NNPP.

LABARAI MASU NASABA

Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

Ana zargin Doguwar da laifin tayar da gobarar a ofishin a ranar Lahadi 26 ga watan Fabarairu, 2023 wanda hakan ya yi sanadin ƙona wasu mutane da ke cikin ofishin.

Laifukan da ake zargin sa da su sun haɗa da kashe wasu mutum uku tare da raunata wasu mutum takwas a ƙaramar hukumar Doguwa a ranar 26 ga wannan watan nan a lokacin da ake karɓa da bayyana sakamakon zaɓen ɗan majalisar.

An yi ta yaɗa hotuna da bidiyon wasu mutane da ake zargi an harba da bindiga a shafukan sada zumunta, daga nan kuma rundunar ‘yan sandan ta gayyaci ɗan majalisar domin gudanar da bincike kan batun.

Sanarwar ta ce bayan da ɗan majalisar ya ƙi amsa gayyatar ne, rundunar ‘yan sandan jihar ta kama shi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke jihar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN
Manyan Labarai

Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

November 14, 2025
Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki
Labarai

Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

November 14, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

November 14, 2025
Next Post
Me Ya Faru Ga Panda Da Amurka Ta Ara Daga Kasar Sin?

Me Ya Faru Ga Panda Da Amurka Ta Ara Daga Kasar Sin?

LABARAI MASU NASABA

GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 14, 2025
Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

November 14, 2025
Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

November 14, 2025
Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah 

Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah 

November 14, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

November 14, 2025
Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe

Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe

November 14, 2025
Masana’antu Masu Zaman Kansu A Arewa Sun Yi Maraba Da Harajin Kashi 15 Na Shigo Da Man Fetur

Masana’antu Masu Zaman Kansu A Arewa Sun Yi Maraba Da Harajin Kashi 15 Na Shigo Da Man Fetur

November 14, 2025
Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati

Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati

November 14, 2025
Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

November 14, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.