Babbar Kotun Shari’a da ke Bauchi a ranar Laraba ta warware belin fitaccen malamin addinin Musulunci kuma babban limamin masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, Dakta Idris Abdul’aziz tare da umartar a sake kamoshi bisa rashin halartar zaman kotun domin ci gaba da shari’ar tuhumar da ake masa.
Kotun a karkashin mai shari’a Malam Hussaini A. Turaki, ta ki amincewa da bukatar da Lauyan mai kariya ya shigar a gabanta da ke nusar da kotun cewa, sun daukaka kara kan wannan lamarin a kotun daukaka kara da ke Jos don haka ya nemi kada kotun ta cigaba da batu kan shari’ar.
- Ali Nuhu Da Murja Kunya Na Cikin Mutane 150 Ma Fi Tasiri A Intanet A 2023
- Harin ‘Yan Bindiga: Jama’a Sun Yi Zanga-zanga A Kaduna, Sun Nemi Taimakon Sarkin Zazzau
Nan take, lauyan gwamnatin jihar ya soki bukatar tare da cewa ba a bi matakan da suka dace na gabatar da wani batun daukaka kara ba.
Sai dai bayan sauraron muhawarar kowani bangare, Mai shari’a ya cimma matsayar cewa, dole ne wanda ake zargi ya bayyana a gaban kotun domin ci gaba da sauraron karar da ake masa.
Idan za a tuna dai, ana zargin babban malamin ne da furta wasu kalamai da ka iya barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali hadi da tunzura jama’a a jihar. Kodayake, a watannin baya malamin har gidan yari ya je amma daga bisani aka samu belinsa.
A ranar Labarar bayan dawowa ci gaba da sauraron karar, lauyan masu shigar da kara, UB Umar na ma’aikatar shari’a ta jihar Bauchi, ya ce, ba kotu ne ko masu shigar da kara za su gabatar da bukata a madadin wanda ake zargi ba, inda ya ce su din sun gaza yin hakan.
Ya ce, “Mun aike masa da sammaci daban-daban, a bayyane balo-balo ya fito ya ce shi ba zai zo kotu ba, muka sake canza sammacin aka manna a addireshinsa domin ba shi damar zuwa kotu.
“Sannan, akwai bukata wacce lauyansa ya shigar, amma ba a gabatar da ita ba.”
Acewar lauyan, kotu ba ta amfani da jita-jita illa abun da aka zo gabanta aka gabatar, don haka, masu kariya ba su bi matakan da suka dace na cewa sun daukaka kara kan shari’ar ba.
“Don haka kotu ta yi umarnin dole ya zo gabanta ya mata bayanin menene dalilinsa na kin halartar zaman da aka yi ta yi a baya, idan yana da hujja mai karfi na yin hakan shi kenan, nan gaba za mu san abun yi.”
Barista UB Umar ya kara da cewa, “Tun da an mika masa sammaci bai zo ba, mataki na gaba shi ne bai wa jami’an tsaron izinin kamoshi gami da gabatar da shi a zaman da kotun za ta yi mako mai zuwa a ranar 24 ga watan nan.”
Shi kuma a bangarensa, lauyan kariya, Ahmad M Umar, ya ce umarnin kamo malamin ba daidai ba ne domin sun sanar da kotun cewa, wannan shari’ar na gaban kotun daukaka kara, don haka, akwai bukatar kotun shari’ar ta mutunta kotun daukaka kara da ke Jos kafin kowane mataki.
Ya ce, “Mun tunatar da koun cewa soke belin wanda ake zargi ba daidai ba ne, sun yi ne bisa kuskure, saboda batun na gaban kotun daukaka kara.
“Mun tunatar da kotun cewa wannan kes din daga wannan kotun zuwa babban kotu sannan zuwa kotun daukaka kara da ke Jos. Mun gabatar da batun ga wannan kotun da sauran bangarorin da lamarin ya shafa tare da notices har guda hudu. Amma sakamakon shari’un zabukan gwamnoni, kotun daukaka karan ba ta samu damar zaunawa kan lamarin ba.
“Yanzu, kotun daukaka ta sake bayar da rana kuma mun shaida wa wannan kotun muka nemi kada ta yi komai domin mutunta matakin kotun daukaka kara, amma duk da suka haka ta soke belin da umarnin a kamo wanda muke karewa.”
Ya ce, matsayarsu shi ne akwai kes din da ke gaban kotun daukaka kara, kuma kotun daukaka kara na gaba da babban kotu balle kotun shari’a. Ya bada tabbacin cewa za su bi matakan da shari’a ta gindaya.