Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar tsaron farin kaya (DSS) da ta saki Godwin Emefiele, dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) cikin mako daga ko ta mika shi zuwa kotu.
Kotun ta ba da wannan umarni ne a lokacin sauraren kara da Emefiele ya shigar inda ya kalubalanci tsare shi DSS ke yi.
- Yau Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Emefiele Ya Shigar
- Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Neja Ta Umarci Masu Gidaje A Hanyoyin Ruwa Su Tashi
A ranar Asabar 10 ga watan Yuni, 2023 DSS ta kama tare da tsare Emefiele.
Kamen nasa na zuwa ne bayan da shugaba Tinubu ya dakatar da shi tare da bayar da umarnin yin bincike a ofishinsa.
Ana dai zargin Emefiele da yunkurin hana jam’iyyar APC cin zaben da aka kammala na 2023 saboda tsarin rage kudi a hannun jama’a da ya kaddamar ciki har da sauya fasalin naira.
Kazalika, ita ma DSS ta zargi Emefiele da taimaka wa ta’addanci wanda hakan ya sanya ta tisa keyarsa zuwa kotu.