Wata kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a filin hoki da ke babban birnin Kano, ta umarci Abubakar Ibrahim da aka fi sani da G-Fresh, da ya koma gida ya shirya zuwa wajen bikon matarsa da ta yi yaji.
Kotun wadda ta bayyana cewar, tunda shi G-Fresh bai saki matarsa ba, akwai bukatar ya yi bikon ta domin cigaba da zaman aurensu.
Lauyar G-Fresh, Barr Fatima Aliyu ta bayyana cewa, har yanzun wanda ta ke karewa na matukar kaunar matarsa wanda hakan yasa ba zai iya rabuwa da ita ba.
Kotun dai ta umurci G-Fresh 25 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Oktoba da ya sulhunta da matarsa, Sayyada Sadiya Haruna.