Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci shugabancin majalisar dattawa da ya gaggauta janye dakatarwar da ya yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
A lokacin da take gabatar da hukuncin, mai shari’a Binta Nyako, ta ce, dakatarwar watanni shida da aka yi wa Natasha ya yi yawa, kuma ba shi da wata madogara a shari’ance. Kotun ta yi watsi da sashi na takwas na dokar majalisa dattawa da sashi na 14 da na dokokin iko da damarmaki na majalisar.
- Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar Da Natasha A Kotu Kan Zargin Ɓata Sunan Akpabio Da Yahaya Bello
- Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Gidan Sanata Natasha A Kogi
Kotun ta bayyana cewa waɗannan dokoki ba su fayyace tsawon lokacin da za a iya dakatar da ɗan majalisa ba.
Kotun ta ce tunda har ɗan majalisa yana da damar zama a majalisa na kwanaki 181 a kowace shekara, hakan yana nufin dakatar da ɗan majalisa na watanni shida ya saɓawa ƙa’ida sannan an tauyewa waɗanda yake wakilta haƙƙinsu.
Kotun ta kuma ce majalisa tana da damar hukunta duk wani ɗan majalisa da ya yi laifi, amma kuma bai kamata a tauyewa ɗan ƙasa damar samun wakili a majalisa ba.
A ɓangare guda kuma, kotu ta samu Natasha Akpoti-Uduaghan da laifin saɓawa umarnin kotu ta hanyar rubutun zaulaya da ta yi a shafinta na Facebook a ranar 7 ga watan Aprilu, inda take bayar da haƙuri amma ta hanyar zaulaya ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Alpabio.
Kotun ta ce rubutun cin fuska ne ga umarninta, sannan ta umarci Natsha da ta rubuta saƙon bayar da haƙuri a shafukan jarida guda biyu da shafinta na Facebook.
Har ila yau, kotun ta ci tarar Natsha naira miliyan biyar bisa rubutun da ta wallafa a shafin na ta na Facebook.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp