Wata babbar kotu a Abuja, ta umarci Antoni Janar na Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a tare da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), su gabatar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Kore, Bello Bodejo, a gaban kotu.
Mai shari’a Mohammed Zubairu ne, ya bayar da wannan umarni a ranar Talata.
Ya ce AGF da DSS su tabbatar sun gabatar da Bodejo a kotu a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba, don sauraron karar da ke shafar haƙƙinsa.
Umarnin ya biyo bayan buƙatar da lauyan Bodejo, Reuben Atabo (SAN), ya gabatar, inda ya nemi a sake shi bisa tanadin sashe na 33, 34, da 36 na kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Lauyan ya kuma roƙi kotu ta bayar da izinin odar “Habeas Corpus” domin tantance halaccin tsare shi da ake yi.
A ranar 10 ga wata Disamba, sojojin bataliya ta 117 suka kama Bodejo a ofishinsa da ke Nasarawa, bayan wata matsala da ta taso tsakanin makiyaya da wani Janar mai ritaya.
An ce makiyayan sun ƙwace bindigar Janar ɗin suka kuma miƙa shi ga ’yansanda.
Tun farkon shekarar nan, DSS ta kama Bodejo bisa zargin ta’addanci, bayan ya kafa wata tawagar tsaro don sasanta makiyaya da manoma.
Sai dai hukumar leƙen asiri (DIA) ta sake shi a watan Mayu bayan an janye tuhumar kafa ƙungiyar ba bisa doka ba.