Kotu ta wanke tsohon dan kwallon Manchester City Benjamin Mendy daga laifin yi wa wata mata fyade bayan shafe makwanni ana shari’a.
An zargi matashin mai shekaru 28 da kai wa wata mata ‘yar shekara 24 hari a gidansa da ke Motram St Andrew, Cheshire a watan Oktoban shekarar 2020.
Ana kuma zargin Mista Mendy da yunkurin yi wa wata mata fyade, mai shekaru 29.
Hakan na zuwa ne bayan da aka wanke shi daga laifukan fyade shida a wata shari’a da aka yi a baya a watan Janairu.
Dan wasan Dan asalin Faransa ya barke da kuka yayin da alkalin alkalan kotun ya karanta hukuncin da ba shi da laifi bayan shari’ar da aka shafe makonni uku ana yi a kotun Chester Crown da ke Ingila.
Alkalan shari’ar maza shida da mata shida sun tattauna na tsawon awanni uku da mintuna 15 kafin su cimma matsaya.
Alkali Steven Everett ya ce ana iya sallamar Mista Mendy daga tashar jirgin ruwa da yake tsare.
Dan wasan, Mendy wanda kwantiraginsa da Manchester City ya kare a wannan watan, an wanke shi a shari’ar farko da aka yi masa na aikata laifuka shida na fyade da kuma cin zarafi daya, wadanda suka shafi ‘yan mata ko matasa hudu.