Babbar kotun Jihar Kebbi ta daya ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wata tsohuwar matar wani alkalin Majastare Mai Shari’a Muhammad Attahiru Ibrahim Zagga, Farida Abubakar, bisa laifin kashe shi yayin da aka gurfanar da ita a gaban kotun.
Marigayin dai ya mutu ne a sakamakon kashe shi da aka yi a gidansa da ke rukunin gidagen Muhammadu Adamu Aliero, inda aka yanke masa wuya da kuma hannun hagu.
- Gwamnatin Kebbi Ta Ayyana Asabar Ɗin Karshe Wata A Matsayin Ranar Tsaftar Muhalli
- Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Nisanta Kansa Da Kalaman PDP
Da yake yanke hukuncin, babban Jojin jihar, Mai Shari’a Abubakar Umar wanda ya yanke hukunci a kan karar, ya ce kotun ta gamsu cewa wacce ake tuhuma da aikata laifin ce ta aiwatar kamar yadda shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar suka nuna.
“An ga wacce ake kara a karshe tare da marigayin a gidansa da ke Birnin Kebbi, jim kadan bayan haka, an sami gawarsa. Haka kuma Shaidar ta dace ta alakanta wadda ake tuhuma da aikata laifin”.
Hakazalika, kotu ta ce ” Ta gamsu da cewa hujjojin da shaidu 12 suka gabatar a gaban kotu sun bayyana cewa ita ce ta kashe marigayin”.
Har ilayau, “An ga marigayin tare da wacce ake kara su kadai, shaidun da aka gabatar sun kasance masu karfi, ba tare da wata jayayya ba, an sami Hijabinta da jini, haka kuma laifin da aka aikata a daidai lokacin da marigayin ya kusa kara auren wata amarya kamar yadda shaidu suka tabbatar wa kotun”.
Bugu da kari Kotun ta kara da cewa ta gamsu da dukkan hujjojin da aka gabatar a gabanta. Ta tabbatar da cewa wadda ake tuhumar ta shirya kai harin ne da wuka mai kaifi, ko shakka babu yankan wukar ya yi sanadin mutuwarsa.
“Kotu ta yanke miki hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda sashe na 191 a ciki (b) na kundin dokokin Jihar Kebbi ta tanada, za a rataye ki ta wuya har sai kun mutu”.
“Kotu ta kuma yanke miki hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari bisa samun ki da laifin cutar da marigayin kamar yadda sashe na 224 (1) na dokokin Jihar Kebbi ya tanada ko ki biya Naira dubu dari ko duka biyun”.
Mai Shari’a Abubakar Umar ya bayyana cewa, bayan sauraron dukkan bangarorin biyu, a irin wannan yanayi, an kashe marigayin ne a lokacin da yake aiki, (Majastare Attahiru Muhammad Ibrahim Zagga) kuma doka ta tabbatar da babu shakka, irin wannan laifin hukuncin ya zama tilas.
Kotun ta bayyana cewa Farida Abubakar ta aikata laifin ne a ranar 25/8/2022 yayin da aka shigar da manyan tuhume-tuhumen a gaban kotu a ranar 26/7/2023 tare da yanke hukunci a ranar 3/6/2024.
Lauyan da ke tsaya wa wacce ake kara, Mudashiru Sale ya ce “wadda aka yanke wa hukuncin da nake karewa za ta daukaka kara kan hukuncin da aka yanke mata a gaban kotun daukaka kara da ke a Jihar Sakwakkato.”
Lauyoyin da ke gabatar da kara sun gabatar da shaidu 12 tare da gabatar da kayan da za su tabbatar cewa an aikata laifin har guda 8 da suka hada da Hijabi mai dauke da jini, inda kotun ta karbe su a Matsayar shaida yayin da wacce ake kara ta gabatar da shaidu 2 da aka shigar da su a gaban Kotun.