An yanke wa shahararren mawakin nan na Amurka hukuncin daurin shekaru 30 bayan samunsa da laifin yin lalata da kuma safarar mata don yin lalata da su a watan Satumban 2021 bayan shafe kusan makonni shida ana shari’a.
Alkalin kotun, Ann M. Donnelly, ta yanke hukuncin ne a wata kotun tarayya da ke Brooklyn, a birnin New York bayan sauraron wasu shaidu da abun ya shafa kan yadda R. Kelly ya zi zarafinsu.
- Ayyukan’Yan Bindiga: An Rufe Makarantun Gwamnati 19 A Katsina
- Taba Sigari Na Kashe ‘Yan Nijeriya 30,000 Duk Shekkara -WHO
“Kai mutum ne da ke da fa’ida mai yawa – kuma ka shahara a duniya, kana da kudi.
“Kun yi amfani da kaunarsu da burinsu, kuka tsare su a gidanku.
“Kun raba su da iyalansu kuma kun tilasta musu yin abubuwan da ba za su iya ba.”
Masu gabatar da kara sun nemi akalla shekaru 25.
Tawagar lauyoyinsa sun yi jayayya cewa bai cancanci fiye da shekaru goma ba saboda “a halin yanzu ba shi da hatsari ga jama’a”.
Mawakin mai shekaru 55 da duniya, ya shafe watanni a tsare yana jiran hukuncin da aka yanke masa na safarar matan da aka ci zarafinsu a ranar 29 ga watan Yuni.
Kelly ya fuskanci zarge-zarge daban-daban a Chicago kan wasu hotunan lalata da kananan yara.
R. Kelly ya shahara da yin fice a harkar waka tsawon shekaru 30 da suka gabata, inda ya buga kundin wakoki da dama wanda suka sa ya samu daukaka a duniya.
Hukumomi sun kama Kelly a Chicago a cikin 2019 kuma suka mayar da shi New York a watan Yuni 2021.