Wata babban kotu da ke zamanta a Abakaliki ta jihar Ebonyi, ta yanke hukuncin kisa, Lucky Godwin, ta hanyar rataya bayan kama shi da laifin kashe wata mace a cikin dakin wani otel da ke Abakaliki.
Ana zargin Lucky da sace diyar mamaciyar bayan da ya daba wa matar wuka ya kashe ta tare da sayar da yariyar ‘yar shekara biyu a Akwukabi Etche ta jihar Ribas.
- ‘Yan Sintiri Sun Kashe ‘Yan Bindiga 12 A Jihar Taraba
- Dan Bindiga Ya Kashe Kananan Yara ‘Yan Makaranta 36 A ThailandÂ
Lokacin da yake yanke hukuncin, Alkalin kotun, Iheanchor Chima ya zartar da hukuncin kisa ga Godwin.
Babbar mai shigar da kara ta jihar, Misis Ijeoma Aja-Nwachukwu, ta yaba da yadda hukuncin ya gudana.
An yi zargin cewa shi ‘Lucky’ ya dauko mamaciyar matar da yariyar ‘yar shekara biyu daga jihar Enugu kuma dukkaninsu sun sauka a wani otel mai suna Crown Garden Hotel, Abakaliki, inda ya kasheta da wuka.
Wukar wacce makashin ya samu daga hannun mai gadin otel din, Monday Onwe, bayan da Lucky ya ba shi naira dubu talatin domin ya taimaka masa wajen zartar da wannan danyen aikin, daga bisani ya gudu daga Abakaliki bayan faruwar lamarin.
An gano gawar mamaciyar ne bayan kisan nata a shekarar 2018.