Mai Shari’a Alkalin Babbar Kotun jihar Jigawa, ya yanke wa wani tsoho dan shekara 60 mai suna, Dayyabu Madaki, hukuncin daurin rai da rai a gidan gyran hali, kan yi wa wata ‘yar karamar yarinya fyade.
Ko a watan da ya gabata, an gurfanar da Dayyabu a gaban wannan kotun bisa zarginsa da yi wa ‘yar shekara tara da haihuwa fyade bayan ya yaudare ta ya kai ta gidansa da ke kauyen Doro a karamar hukumar Jahun.
- An Cafke Wani Mutum Da Ya Yi Wa ‘Yar Uwarsa Mara Hankali Fyade A Kebbi
- Kotu Ta Wanke Bejamin Mendy Daga Zargin Fyade
Alkalin da yake yanke hukuncin ya sanar da cewa, laifin na fyade ya sabawa sashen doka ta 282 (1) na sokokin jihar ta shekarar 2012, inda kuma sashe na 3 na dokar ya tanadi yin hukunci.
Dayyabu ya amsa laifinsa kan tuhumar da aka yi masa, inda kuma dan sanda mai gabatar da kara ya gabatar wa da kotun wasu hujjoji biyu, da suka hada da bayanan ‘yansanda da kuma rahoton da Asibiti ya fitar a kan lafiyar yarinyar.