Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke wa wata mata mai shekaru 20, Faith Joseph, hukuncin shekaru huɗu a gidan yari saboda safarar wata budurwa mai shekaru 21 zuwa Burkina Faso domin ƙaruwanci.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a M. N. Yunusa, ya bayyana cewa masu shigar da ƙara sun tabbatar da laifin da shaidu tabbatattu, inda ya yanke mata shekaru biyu a kowane laifi cikin tuhume-tuhume biyu, ba tare da zaɓin tara ba.
- NAPTIP Ta Kama Mutum 5 Da Ake Zargi Da Safarar Mutane A Filin Jirgin Saman Abuja, Ta Ceto Mutane 24
- NAPTIP Ta Ceto ’Yan Mata 9 Masu Juna Biyu A Abuja
Lauyan hukumar NAPTIP, Hassan Nuraddeen, ya shaida wa kotun cewa Faith ta aikata laifin ne tare da wata mace mai suna Grace James, wadda tuni ta tsere, inda suka yi safarar wata budurwar daga unguwar Panshekara, zuwa Burkina Faso ta hanyar Legas da Kwatano.
Nuraddeen ya ce an gabatar da bayanin amsa laifin Faith a matsayin hujja, wanda ya tabbatar da laifin safarar mutane da karya dokar safarar mutane (Prohibition Enforcement and Administration) Act, 2015, sashi na 26(1) da 18.
Lauyan wacce aka yanke wa hukunci, M. B. Isah, ya roƙi sassauci saboda ƙarancin shekarunta da nadamarta, amma kotu ta dage kan cewa hukuncin zai zama darasi ga sauran masu hannu a safarar mutane, domin hana maimaita irin wannan aika-aika.














