Wata babbar Kotu da ke garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta yanke wa wata bazawar Ba’amurkiyar bogi mai suna, Aderibigbe Sheu, hukuncin zama a gidan gyara hali har na tsawon shekaru uku.
Matar wacce daliba ce a jami’ar (KWASU) mallakar jihar Kwara, ta bayyana ne a wani hoto inda ta tsaya a wani Gini na kasar Amurka don damfarar Jama’a a matsayin bazawara.
- Sabon Yunkurin Amurka Kan Batun Taiwan Aikin Banza Ne
- EFCC Ta Cafke ‘Yan Damfara A Yanar Gizo 39 A Oyo
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da matar a gaban kotun kan zarginta da tuhumar aikta laifin damfara.
A cikin sanarwar da kakakin hukumar ta kasa, Wilson Uwujaren, ya fitar a ranar Alhamis ya ce, matar ta amsa laifin da ake zarginta da aikata wa.
Bayan ta amsa laifin, lauyan hukumar EFCC, Rasheedat Alao, ta gabatar wa da kotun wasu kayayyakin da aka samu matar da suka hada da wayar hannu da Kwamfiyuta da kuma sauran kayan aikata laifi wadanda kotun ta amince da su a matsayin hujja.
Alkalin kotun, mai Shari’a Sani, ya nuna gamsuwarsa kan hujjojin da aka gabatar wa kotun, inda ya yanke wa matar hukuncin zama a gidan gyran haki na tsawon shekaru uku ko kuma biyan tarar naira dubu dari tara da tamanin da biyu da naira dari hudu da uku (N982, 403).