Kotun hukunta laifukan lalata da maza da mata a Jihar Legas ta yanke wa wani malamin Islamiyya, Adam Farouk, hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifin lalata da dalibansa takwas ‘yan kasa da shekaru shida.
Mai shari’a Soladoye Abiola, ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da babu shakka a cikin tuhume-tuhume takwas da suka hada da cin zarafi ta hanyar yin lalata da malamin ya yi, ya gamsu.
- Kaso 6 Na Al’umma Ne Kadai Ke Ganin Duniya Za Ta Kasance Karkashin Ikon Amurka
- Wata Mata Ta Yi Wuf Ta Aure Saurayin Diyarta A Kano
Mai shari’a ya bayyana malamin a matsayin wanda bai da tarbiyya kuma abin kunya ga Addinin Musulunci, inda ya bayyana cewa an tabbatar da hujjojin da suka nuna yadda ya yi amfani da hannunsa wajen lalata daliban.
Wata shaida ta ce wanda ake tuhumar ya umarci yaran da su juya baya yayin da yake lalata su da yatsansa.
“Ana sa ran ya koya wa dalibansa dabi’u, da’a da kuma tarbiyya, amma sai aka samu akasin haka. Abin da ya aikata abun ki ne.
“An yanke wa wanda ake tuhuma da dukkan tuhume-tuhumen kuma an yanke masa hukuncin daurin rai da rai a kan kowanne daga cikin laifuka takwas amma hukuncin zai gudana a lokaci guda.”
Kazalika, alkalin ya bayar da umarnin a rubuta sunan wanda ake tuhumar a cikin rajistar masu aikata laifuka ta jih6ar Legas.