Wata kotu a kasar Malawi ta yanke hukuncin daurin rai da rai tare da aiki mai tsanani a kan wasu mutane biyar saboda samunsu da laifin kashe wani zabiya a shekarar 2018.
An gano gawar mutumin ne mai suna MacDonald Masambuka, a wani dan rami da aka binne ta, bayan ya yi makonni ba a gan shi ba.
- Yadda Matafiya 18 Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Hadarin Mota A Neja
- Na Yi Babban Kuskuren Zabar Atiku Mataimakina A 1999 – Obasanjo
Wadanda aka yi wa hukuncin a birnin Blantyre, sun hada da wani limamin cocin Katolika da dan sanda da kuma wani dan uwan zabiyan.
A watan Afrilu ne kotun ta same su da laifin kisan gillar.
An danganta kisan zabiya da tsafi, inda bokaye da wasu masu maganin gargajiya ke karyar cewa ana amfani da sassan jikinsu ne domin samun nasara ko dukiya.
Hukumomin kasar ta malawi sun ce tun shekarar 2014 an kai wa zabiya 170 hari, da suka hada da sama da 20 da aka kashe.
A Malawi kisa ko satar zabiya da nufin yin tsafi da su na neman zama ruwan dare, lamarin da ya fara damun gwamnatin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp