Mai shari’a James Omotosho na babbar Kotun tarayya da ke Abuja ya yi watsi da ƙarar da aka shigar don ƙalubalantar matakin Shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas a ranar 18 ga Maris, 2025.
A watannin baya ne dai gwamnatin tarayya ta dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mambobin majalisar dokoki na jihar na tsawon watanni shida, inda shugaban ƙasar ya naɗa mai kula da harkokin jihar mutum ɗaya tilo.
- Majalisar Dokokin Ribas Za Ta Binciki Tsohon Kantoman Riƙo Ibok-Ete Ibas
- Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnan Ribas, Fubara Ya Ziyarci Tinubu A Fadar Gwamnati A Abuja
Masu ƙarar guda biyar ƙarƙashin jagorancin Belema Briggs sun yi iƙirarin cewa matakin ya tauye musu ƴancinsu, amma a hukuncin da ya yanke ranar Alhamis, Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa ba su da hurumin shigar da ƙarar, domin irin wannan batu na ƙarƙashin ikon kotun ƙoli.
Kotun ta ƙara da cewa masu ƙarar ba su nuna cewa suna daga cikin ƴan majalisar zartarwa ko dokokin jihar ba ne, haka kuma ba su tabbatar da wata cuta da ta fi wadda sauran jama’ar jihar suka sha ba. Bugu da ƙari, ba su sami sahalewar babban lauyan jihar Ribas ba kafin su shigar da ƙarar ba.
Mai shari’a Omotosho ya jaddada cewa dalilin da Shugaba Tinubu ya bayar na ayyana dokar ta-ɓacin don guje wa rikici da rushewar doka da oda bai samu wani ƙalubale ba. Don haka kotun ta bayyana ƙarar a matsayin marar tushe kuma bata da amfani, kasancewar masu ƙarar ba su da sahihin wakilci daga al’ummar jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp