Wata babbar kotun tarayya da ke Jihar Legas, ta yi watsi da wata kara da aka shigar gabanta na neman cire rubutun ajami a takardun kudin Nijeriya.
Barista Malcolm Omirhobo ne ya shigar da karar, inda yake kalubalantar Babban Bankin Nijeriya (CBN), kan kotu ta umarce shi domin cire rubutun ajami na harufan Larabci daga takardar Naira.
- Southgate Ya Ajiye Aikin Horas Da Ingila
- An Kaddamar Da Harkar Sada Zumunta A Tsakanin Yaran Sin Da Na Afirka
Kotun ta yi watsi da karar a ranar Talata, inda mai shari’a Yellim Bogoro, ya nuna cewa wanda ya shigar da karar ya gaza bayar da hujjoji da za su nuna cewa CBN ya sanya rubutun ajami da wata mummunar manufa.
Kafin zartar da hukuncin, kotun ta ce Nijeriya kasa ce mai cikakken ‘yanci, inda ya jaddada da cewa babu fifita wani addini ko kabila.
Tun a 2020 aka fara shari’ar, wanda sai a yau Talata babbar kotun da ke Lagos ta zartar da hukunci.
Mai shari’a Yellim, wanda ya yi watsi da karar ya kara da cewa kotun ta dogara ne da shari’ar Cif Gani Fawehinmi da Akilu da aka yi a shekarar 1998.
Kotun ta ce yayin da Cif Omirhobo ke da gurbi don sauraron kararsa amma kuma ya kasa bayar da isasshiyar hujja da za ta nuna cewa tsarin da CBN ya yi don ci gaba da amfani da rubutun ajami kan takardun Naira da rubutun Larabci, an yi shi ne da muguwar manufa.
Sauran wadanda suke cikin shari’ar sun hada da kungiyar kare hakkin Musulmi karkashin daraktanta, Farfesa Ishaq Akintola da kuma Umar Kalgo, wani fitaccen lauya mazaunin Jihar Kebbi.
Babban Daraktan kungiyar kare hakkin Musulmi , Farfesa Ishaq Akintola, bayan yanke hukuncin ya ce wannan nasara ce mai cike da albishir ga Musulmi da masoya Musulunci a fadin Nijeriya.
A martanin da ya mayar kan hukuncin, Mista Omirhobo ya ce ya nemi a ba shi kwafin hukuncin kuma zai yi nazari don daukar mataki na gaba.
Da yawa dai ba su fahimci cewa kafin zuwan turawan mulkin mallaka galibi ana amfani ne da harufan Larabci domin rubuta harsunan Afirka da ake kira “Ajami.”