A ranar Talatar da ta wuce ce wata kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta kori karar da aka shigar kan domin neman a cire Alkali Baba Usman daga matsayinsa na shugan rundunar ‘yansanda.
A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Omotoso ya kafa hujja da sashi na 7 (6) na dokokin ‘yansanda na shekara ta 2020 wanda ya bayyana shekara hudu a matsayin wa’adin da za a yi a ofishin shugaban ‘yansandan.
- Da Dumi-Dumi: Sergio Ramos Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Sifaniya Kwallo
- Xi Jinping Ya Ba Da Umarni A Yi Namijin Kokarin Ceto Wadanda Suka Bace Sakamakon Rugujewar Mahakar Ma’adinin Kwal A Jihar Mongoliya Ta Gida
Haka kuma mai shari’a Omotoso ya ce wanda ya shigar da wannan karar ba shi da hurunin da zai shigar da karar.
Sannan ma ya kasa kawo hujja kan zargin da yake yi.
Idoko, wanda ya shigar da kara ta hanyar lauyansa mai suna Chief James Ogwu Onoja, SAN.
Yanzu haka dai an kori wannan kara mai lamba FHC/ CS/.
An Kashe DPO Da Wasu ‘Yansanda a Jihar Anambra
‘Yan bindiga sun ofishin ‘yansanda na Isiowulu Awada, da ke karamar hukumar Idemili ta Arewaa jihar Anambra inda suka kasheDPO, da wasu mutun biyu.
‘Yan bindigar sun yi dirar mikiya a ofishin ‘yansandan kuma nan take suka bude wuta.’Yansandan sun mayar da martini tare da taimakon sojoji kuma suka samu nasarar kashe mutum uku daga cikinsu.
Wannan DPO da aka kashe, bai ma dade da fara aiki ba da wani sifeto. An kai wannan harin ne , jim kadan bayan wani hari da aka kai ofishin ‘yansanda na 3-3 da ke karamar hukumar Oyi, wanda kuma a wannan harin ‘yansandan suka samu nasarar kashe ‘yanta’adda guda shida.
Wata majiya daga wannan yanki da abin ya faru, ta bayyana cewa, ‘yan bindigar sun bude wuta lokacin da suka tunkari ofishin ‘yansandan kuma sun shafe awanni suna harbi. Bayan wannan kuma ‘yan bindigar sun kai hari ofishin ‘yansanda da ke Isiowulu.
A nan kuma an yi bata-kashi da ‘yansanda sun harbi mutum uku kuma sun kace bindiga AK-47.