Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa za ta yanke hukunci kan karar da ‘yar takarar jam’iyyar APC, Aishatu Dahiru Binani ta shigar, inda ta ke kalubalantar nasarar Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a 28 ga watan Oktoba, 2023.
Idan dai za a iya tunawa, jam’iyyar APC da ‘yar takararta ne suka shigar da kara kan ayyana Gwamna Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
- Gwamnatin Tarayya Ta Karbi ‘Yan Nijeriya 108 Da Suka Makale A Nijar
- Kwastam Za Ta Rungumi Aiki Da Fasahar Zamani Domin Habaka Harkokinta – Adeniyi
APC ta yi zargin karya dokokin zabe da kuma tafka magudin zabe. APC da Binani a cikin kokensu, sun bukaci kotun ta tabbatar da sanarwar da kwamishinan zabe na jihar, Hudu Yunusa Ari ya yi wanda ya ce, APC ce ta lashe zaben.
A bangaren Jam’iyyar PDP da dan takararta, Fintiri, sun gabatar da bukatarsu a gaban kotun inda suke neman kotun da ta yi watsi da karar da APC da ‘yar takararta suka shigar.