Babban magatakardar kotun daukaka kara, Umar Mohammed Bangari, ya yi karin haske kan cece-kucen da ake barke dangane da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke kan rikicin zaben gwamnan Jihar Kano.
Magatakardar, a martanin da ya mayar dangane da cece-kucen da aka yi a kan kundin hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, ya ce tuntuben alkalami aka samu.
- Lauyoyi Sun Bukaci Kotun ECOWAS Ta Haramta Takunkumi Kan Nijar
- Gwamna Nasir Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Naira Biliyan 250 Ga Majalisar Dokokin Kebbi
Ya ba da tabbacin cewa za a gyara kuskuren da zarar bangarorin da suka shigar da kara sun mayar da kwafin da aka ba su.
Ya ja hankalin ’yan jarida game da doka ta 23 da doka ta 4 kan kundin kotun daukaka kara, wadda ta bai wa kotu ikon gyara duk wani kuskuren da yi game da hukuncin shari’a.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Haruna Isah Dederi, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa, hukuncin kotun daukaka kara da ta yanke ya tabbatar da zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf, sabanin yadda alkalai suka bayyana a kotun.
Tun daga wannan lokacin ne aka fara tafka muhawara kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke wanda ya tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Kano ta yanke a baya wadda ta soke zaben Gwamna Yusuf na jam’iyyar NNPP.